An kai hari kan wani Otal a kasar Libya

Hari a kasar Libya Hakkin mallakar hoto ALI TAWEEL
Image caption Hari a kasar Libya

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani babban otal a Tripoli, babban birnin Libya, bayan sun tayar da bam cikin wata mota a waje.

Wani jami'in tsaron kasar yace masu gadin otal din 3 ne suka mutu yayin da 2 daga cikin 'yan bindigar suka kutsa cikin Corinthia otal da safiyar Talata.

Rahotannin da ba a tabbatar ba na cewa akwai yiwuwar 'yan bindigar suna yin garkuwa da wasu mutane.

Corinthia dai shahararren otal ne da ya kasance matattarar manyan 'yan kasuwa da jami'an diplomasiyya da kuma jami'an gwamnati.

Kungiyar IS dake Libya ta ce ita ta kai harin a shafinta na twitter.