Mexico: an samu karin haske kan batar dalibai

Image caption Masu zanga zanga sun ki amincewa da bayanan dake nuna an kashe daliban ne

Babban lauyan gwamnatin Mexico ya ce yana da sheda ta hakikani a game da tabbacin abinda ya faru da dalibannan 43 da suka bace a Guerreo cikin watan Satumban bara.

Jesus Murillo Karam ya sanar da hakanne kwana daya bayan dubban mutane sun yi zanga zanga a birnin Mexico, inda suka bukaci a sanar dasu ainihin abinda ya faru da daliban.

Babban lauyan ya ce an kashe dalibanne sannan aka kone gawarwakinsu a wani wuri da ake zubar da shara.

Mista Karam ya ce shi da abokan aikinsa sun zanta da kimanin mutane 100 da suka hada da wasu daga cikin gungun 'yan daban da suka kashe daliban.

Ya kuma musanta zargin cewa sojojin kasar suna da hannu a bacewar daliban.

Daliban sun bace ne bayan sun shiga wata zanga zanga a garin Iguala a watan Satumba.