Ghana ta cire fastocin 'yan siyasar Nigeria

Image caption Ghana ta ce ta cire hotunan ne domin gudun rikici

Gwamnatin kasar Ghana ta bayar da umarni a cire hotunan 'yan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyun PDP da APC da aka kafa a wasu wurare a kasar.

Gwamnati ta ce ta bayar da umarnin ne domin kada hakan ya janyo rikici.

Ta kara da cewa babu tabbas kan sakamakon zaben da za a yi a Najeriya don haka, a cewarta, idan rikici ya barke a zaben zai iya shafar kasar ta Ghana, tunda dai akwai masu ra'ayoyin jam'iyyun na Najeriya a can.

Su ma 'yan jam'iyyun na Najeriya da ke Ghana sun tabbatar wa BBC cewa ba su nemi izinin hukumomin kasar ba gabanin sanya wadannan hotuna na 'yan takarar Najeriyar.