Amurka na fuskantar guguwar dusar kankara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An soke tashin jirage fiye da dubu shida a fadin yankin arewacin Amurka

An ayyana dokar ta-baci a jihohi shida na Amurka, inda ake tsammanin guguwar sanyi ta Juno za ta shafi mutane miliyan sittin.

Birnin New York da wani yanki mai girma a arewa maso gabashin Amurka da gabashin Canada na fuskantar dusar kankara da iska mai karfi da ta kusa kai wa mahaukaciyar guguwa.

Ana dai tsammanin guguwar Juno za ta haifar da dusar kankara mai tudun da ya kai centimita 90.

An sanya dokar hana tuki a wasu unguwannin da ke kudancin jihar New York, yayin da a birnin na New York kuma aka hana motocin da ba na aikin agajin gaggawa ba yawo.