Oxfam ta nemi a tallafa bayan kawar da Ebola

Hakkin mallakar hoto Oxfam
Image caption Akwai alamun cewa cutar Ebola ta fara sauki a kasashen da ta addaba a Yammacin Afrika

Kungiyar agaji ta Oxfam ta yi kira da a yi wani gagarumin shiri domin farfado da kasashen da cutar Ebola ta shafa, bayan an kawar da cutar.

Shugaban Oxfam, Mark Goldring, ya ce sai da lokaci ya kure sannan duniya ta farga da cutar ta Ebola.

Amma a cewarsa a yanzu babu wani uzuri da zai sa ba za a taimaka wa mutanen da cutar ta gurgunta rayuwarsu ba, tare kuma da farfado da tattalin arzikin kasashen.

Kungiyar dai na bukatar a yi wani taro domin tara miliyoyin daloli da za a yi amfani da su a shirin, tana mai yin hannunka-mai-sanda ga irin shirin agajin da nahiyar Turai ta yi bayan yakin duniya na biyu.