Thailand za ta sanya dokokin amfani da jirage marasa matuka

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga Thailanda na cewa Ma'aikatar sufuri ta Thailand na duba yiwuwar haramtawa dukkanin jirage marasa matuka da basu da lasisi tashi

An ambato ministan sufurin kasar yana cewa duk wadanda aka kama suna tuka jiragen da basu da lasisi ka iya fuskantar zaman gidan yari na shekara guda da kuma tara ta $1229

Cikin irin abubuwan da ma'aikatar ta gabatar har da yiwuwar haramta makala na'urorin daukar hoto ga jirage marasa matukan, banda dalilai na harkokin kasuwanci

Sashen kula da harkokin sufurin jiragen sama shi ne ke wadannan tsare tsare.

Za kuma a tura su zuwa taron ministoci domin a amince da su.

Sannan za su iya soma aiki kama daga wata mai zuwa

Masu daukar hoto da masu shirya fina finai da kuma 'yan jarida za su iya amfani da jiragen da aka makalawa na'urorin daukar hoto amma banda wasu

Ma'aikatar sufuri ta Thailand ce zata sa ido, ta kuma amince da duk wata bukata ta amfani da jirage masara matuka daga 'yan kasuwa da kuma sauran daidaikun jama'a

Thailand na daya daga cikin kasashen duniya dake neman takaita abubuwan da masu jiragen za su iya y da su.