Apple ya ci gagarumar riba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Apple ya ce yana fuskantat koma baya a cinikin Ipad

Kamfanin Apple ya ci ribar $18bn wadda bai taba cin irinta ba a rubu'in karshe na shekara.

Kamfanin, wanda ke da shalkwata a birnin California na Amurka, ya ce ya samu ribar ne sakamakon karbuwar da wayoyinsa na i-Phone 6 da 6 plus suka yi a kasuwa.

An fi sayen wayoyin Apple a kasar China, domin kuwa alkaluma sun nuna cewa, a karon farko, cinikin da Apple ya yi na wayoyin iPhone a kasar ya zarta wanda ya yi a Amurka.

Sai dai Apple ya ci gaba da fuskantar koma baya a cinikin iPad, inda ya fadi da kashi 18 cikin 100 a bara.