INEC ta shirya wa masu niyyar yin magudi - Jega

INEC
Image caption INEc ta ce a shirye take ta gudanar da zabe a watan Fabrairu

Shugaban hukumar zaben Nigeria, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce dukkan wadanda suke sayan katunan zaben mutanen domin yin magudi ba za su kai labari ba.

Farfesa Jega ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC a Abuja.

Bayanai na nuna cewa wasu na ci gaba da sayen katunan zabe na din-din-din daga hannun jama'a domin yin magudin zabe.

Shugaban na INEC ya kara da cewa hukumar sa a shirye ta ke ta gudanar da zabe inda ya ke cewa zaben zai fi na shekarar 2011 inganci.

"Wannan kati na din-din-din da muka nace a yi amfani da shi, za mu kawo wata na'ura wacce za ta karanta mana cewa duk wanda aka sayi katinsa, wannan na'urar za ta gano cewa katin ba na sa ba ne." In ji Jega.

Farfesa Jega ya kara da cewa idan aka rage irin wannan magudin, ba bu shakka za a smau inganci da sahihancin zabe.