Jagorar kungiyar Pegida ta yi murabus

Shugabar kungiyar Pegida  Katrin Oertel Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar kungiyar Pegida Katrin Oertel

Katrin Oertel ta dare shugabancin kungiyar ce a makon da ya gabata bayan da wasu jaridu suka wallafa hotuna da ke nuna wanda ya kirkiro kungiyar, Lutz Bachmann, yana kwaikwayon Hitler.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook tace Katrin Oertel ta sha fuskantar barazana da rashin jituwa.

Kafafen yada labaru na Jamus na cewa ta yi murabus din ne saboda yadda tasirin Mista Bachmann ke cigaba da wanzuwa a cikin kungiyar.

Pegida dai ta sha shirya zanga-zangar adawa da musulunci inda kimanin mutane 25,000 ke halarta a Dresden.