Boko Haram: Chadi ta kwato Malamfatori

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A bara 'yan Boko Haram suka kwace garin na Malumfatori

Rahotanni daga Chadi na cewa sojin kasar sun kwato garin Malamfatori na jihar Borno daga hannun 'yan Boko Haram.

Garin dai yana yammacin kogin Chadi ne da kuma iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Nijar.

A bara ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kwace shi lokacin da suka kai hari a yankin.

A makon jiya sojin Nigeria sun ce takwarorinsu na kasar Chadi za su rika tsallakawa cikin Najeriyar domin kai wa 'yan Boko Haram hare-hare.