An jefi ayarin motocin Jonathan a Jalingo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo

An jefi ayarin motocin shugaba Goodluck Jonathan a Jalingo babban birnin jihar Taraba lokacin da ya je kamfe a jihar.

Masu jifan na zargin Mr Jonathan da gazawa wajen kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram.

An rotsa tagogin motoci da dama a cikin ayarin kafin 'yan sanda su yi amfani da barkonon tsohuwa su tarwatsa dandazon mutanen.

Akwai dubban 'yan gudun hijira a Yola sakamakon kwace garuruwansu da 'yan Boko Haram suka yi.

A biranen Katsina da Bauchi ma an jefi ayarin motocin kamfe din Jonathan lokacin da ya je zawarcin masu kada kuri'a.

'Yan makonni suka rage kafin gudanar da zaben shugaban kasa a Nigeria inda zai yi zafi tsakanin Mr Jonathan na jam'iyyar PDP da Janar Buhari na jam'iyyar APC.