Ma'aikatan mai na yajin aiki a Nijar

matatar man Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption matatar man Nijar

A yau Talata, ma'aikatan matatar man petur ta Nijar suka fara wani yajin aiki na kwanaki uku. Suna yajin aikin ne domin neman wasu hakkokinsu daga wannan matatar man petur wadda ta hadin gwiwa ce tsakanin gwamnatin jamhuriyar ta Nijar da kampanin mai na China CNPC.

Wannan shi ne karo na biyu da suke shiga yajin aikin a wannan wata.

Ma'aikatan kungiyar ta SORAZ na korafin cewa ana biyan takwarorinsu 'yan kasar Sin albashin da ya ninka nasu sau goma.