Zaben Nigeria: Haɗa siyasa da Addini

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar 14 ga watan Fabarairu za ja zare tsakanin Jonathan da Buhari

Zaman zullumi na karuwa a Nigeria a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zabukan kasar a watan Fabarairu.

Wasu na fargabar cewa kasar na kan siradi saboda bambamce-bambamcen da ke tsakanin al'umma sakamakon takarar shugabancin kasar tsakanin Kirista daga kudancin kasar, Goodluck Jonathan da kuma Musulmi dan arewacin kasar, Muhammadu Buhari.

Zaben zai kasance mai zafin gaske, amma kuma abin tambaya shi ne ko masu zabe sun mai da hankali a kan addinnin 'yan takara ?

"Idan shugaba Kirista bai cancanta ba, to ba zan zabe shi ba don yana Kirista," in ji Arome Okwori da ke zaune a Jos.

Ya kara da cewar "Amma idan shugaba Musulmi ba zai tabbatar da 'yancin addinni ba, watakila in zabi Kirista."

A cewarsa Kiristoci da dama suna jin tsoron Janar Buhari zai aiwatar da shari'ar Musulunci a kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai majami'u da dama a Nigeria

Kakakin jam'iyyar APC, Lai Mohammed ya ce "Janar Buhari ya yi amanna da kafa Nigeria bisa rarrabe tsakanin harkokin gwamnati da na addinni."

"Ba shi da tsatsaurar ra'ayin addinni, sharri kawai ake musa," in ji Lai.

'Jonathan da Malaman Coci'

Akwai 'yan Nigeria wadanda ke cewa Shugaba Jonathan yana da kusanci da manyan fasto-fasto masu dinbin arziki da suke da rassan coci da dama a fadin kasar.

'Yan Nigeria na da zumudi a kan addini kuma sakamakon zabukan bana zai nuna hakan a arewacin kasar, wanda galibin al'ummar yankin Musulmai ne a yayin da a kudu nan ne galibin Kiristoci su ke.

"Ba za ka iya raba dan Nigeria da kishin addini ba," in ji Khadijah Hawaja Gambo.

Matar ta ce "Muna bukatar shugaban da zai magance matsalar tsaro kuma a samu zaman lafiya a tsakanin al'umma."

'Addu'o'in zaman lafiya'

Image caption Akwai Masallatai masu yawa a arewacin Nigeria

Son zuciyar 'yan siyasa ne da kuma na jam'iyyun siyasa ke kara janyo zaman dar-dar a kan batun zabe.

Ana ta yin addu'o'in zaman lafiya a Nigeria a Masallatai da Majami'u domin a yi zabe cikin kwanciyar hankali.

Dabara ta rage ga 'yan siyasa su daina dumama yanayin da ake ciki su tabbatar da cewa ba a samu rikici ba a kasar sakamakon bambamce-bambamcen addini.

Akwai hadari sosai idan aka saka addini a cikin siyasa, kuma bayan zaben 2011 an kashe mutane kusan 800 a arewacin kasar, bayan da aka sanar da cewa Janar Buhari ya fadi zabe.