Tarayyar Afrika na taro a kan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tarayyar Afrika ta bukaci a girke sojoji 7500 domin yakar Boko Haram

Kungiyar Tarayyar Afrika tana gudanar da taro a Addis Ababa domin tattauna matsalolin nahiyar da suka hada da batun rikicin Boko Haram.

A zaman da kwamitin tsaronta ya gudanar ranar Alhamis, Tarayyar Afrikan ta yi kiran a samar da dakaru 7500 a rundunar hadin gwiwa tsakanin wasu kasashen yammacin Afrika domin yaki da Boko Haram.

Shugabar hukumar kungiyar Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce kisan gillar da kungiyar Boko Haram ke yi wa mutane ya wuce tunani.

Ta ce ci gaba da kaddamar da hare hare da kungiyar ke yi a Najeriya da yankin tabkin Chadi da iyakar Chadi da Kamaru da kuma lardinan arewacin Kamaru, yana iya haddasa babbar fitina a yankin baki daya, da jefa jama'a cikin bala'i.

Rikicin Boko Haram wanda a farko yake matsala ta Najeriya ita kadai, yanzu ya zamo matsalar da ta shafi kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriyar.

Fiye da mutane 13,000 suka mutu a hare haren kungiyar ta Boko Haram tun daga 2009, sannan fiye da miliyan daya suka rasa matsugunnai.