Buhari ya janye daga muhawara - APC

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jam'iyyar APC ta yi zargin ba za a yi mata adalci ba a wurin muhawarar

A Najeriya, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jami'yyar hamayya ta APC ya ce jam'iyyar ta janye daga mahawarar 'yan takarar shugaban kasa da mataimaki da kungiyar kafafen yada labarai BON ta shirya.

A cikin wata sanarwa, kwamitin ya ce 'yan takararsu ba za su shiga mahawara ba da aka shirya yadawa ta gidajen rediyo da talabijin da ke karkashin kungiyar ta BON.

Kwamitin ya ce ya dauki matakin ne ganin yadda kafafen yada labaran, wadanda yawancinsu na gwamnati ne ko kuma suna da alaka da gwamnatin PDP suke yada kamfe da tallace-tallace na batanci ga jamiyyar ta APC.

Sai dai daya daga cikin jagororin hukumar ta BON, Malam Ladan Salihu ya musanta zargin da jam'iyyar APC ta yi, inda ya ce wannan ba shi ne karon farko da suka shirya mahawarar ba duk da kasancewarsu kafofin gwamnati