Cinikin jarirai: Kotun Nijar ba ta da hurumin shari'a

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hama Amadou ya tsere daga kasar ta Nijar

A Jamhuriyar Nijar, alkalin da ke shari'ar matar tsohon shugaban majalisar dokokin kasar, Hama Amadu, ya ce ba shi da hurumin yi mata shari'a.

An zargin matar Hama Amadu da kimanin mutane 30 da hannu a cinikin jarirai daga Najeriya zuwa kasar ta Nijar.

Lamarin dai ya sa Hama Amadou ya tsere daga kasar ta Nijar.

Alkalin ya tabbatar da hakan ne ranar Juma'a a Yamai, babban birnin kasar.

Lauyoyin mutanen da ake zargi dai sun gamsu da wannan hukunci.

A ranar biyu ga watan Janairu ne dai mutanen suka gurfana gaban alkalin, amma lauyoyinsu suka dage kan cewa alkalin, da ita kanta kotun ba su da hurumin yin shara'r.

A yanzu dai ya rage wa hukumomin, ko dai su yi watsi da karar ko kuma su daukaka kara.