Mugabe ya zama sabon shugaban AU

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mugabe ya soki Turawan mulkin mallaka

Shugabannin kasashen Africa sun zabi shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, a matsayin sabon shugaban kungiyar kasashen na Africa, AU.

Shugabannin sun yi zaben ne a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia ranar Juma'a.

Mista Mugabe, mai shekaru 90 a duniya, shi ne shugaban da ya fi tsufa a cikin shugabannin nahiyar.

A lokacin da yake jawabi bayan zaben nasa, Mista Mugabe ya caccaki Turawan mulkin mallaka.

Zai yi shekara daya ne a matsayin shugaban kungiyar ta kasashen Africa.