Sojin Chadi sun yi luguden wuta a Gamboru

Wasu sojojin Chadi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu sojojin Chadi

Wani wanda yake garin na Fotokol ya shaida wa BBC cewa ya ga jiragen yaki masu dauke da tambarin kasar Chadi suna shawagi a sararin samaniya, sannan kuma suna ta ruwan bama-bamai a kan garin.

Gamboru-Ngala dai yana daya daga cikin kananan hukumomin jihar Borno da 'yan kungiyar Boko Haram suka mamaye a 'yan watannin da suka gabata.

Sakamakon haka al'ummar garin sun yi gudun hijra zuwa wasu garuruwan kasashe makwabta da suka hada da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Tuni dai kasar Chadi ta lashi takobin kawo karshen tashin hankalin na yan kungiyar Boko Haram a arewacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar tarrayar Afirka ta amince da kafa wata rundunar hadin gwiwa tsakanin kasashe biyar da suka hada da Najeriya da Nijar da Kamuru da Chadi da kuma kasar jumhuriyar Benin domin yaki da ta'addanci a iyakokin