Masar ta haramta kungiyar Hamas

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kotun ta kuma sanya kungiyar Hams din cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Hamas dai ita ce babbar mai karfin iko a Gaza.

Jami'an Masar suna zargin cewa ana fasakwaurin makamai daga yankin Gaza zuwa cikin arewacin Sinai inda Masar din ke gwagwarmaya da masu tada kayar baya.

Hamas dai ta soki hukuncin kotun da cewa siyasa ce kawai.