Merkel: Ba za a yafe wa Girka bashi ba.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wannan lamarin dai ya sa murna ta koma ciki ga fatan da sabuwar gwamnatin Athens ke da shi.

Mrs Merkel ta shaidawa wata jaridar Jamus cewa ba ta hangen Girka za ta sami wani tallafin kudi a nan gaba saboda bankuna da hukumomin bada bashi masu zaman kansu sun riga sun yafewa kasar biliyoyin daloli a baya.

Kwamishinan kula da harkokin kudi na kungiyar tarayyar turai ya yi alkawarin zai yi bakin iyawarsa domin ganin Girka ta cigaba da kasancewa cikin kasashe masu amfani da kudin euro.