Za a halasta zubda ciki a Chile

Shugabar Chile Michelle Bachelet Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A kasar Chile dai hukuncin shekaru biyar ne ga duk wadda aka samu da zubda ciki.

Shugabar kasar Chile Michelle Bachelet ta sanar da wani shiri da zai kawo karshen haramta zubda ciki a al'umar da ke bin darikar Roman Katolika.

A wata sanarwa da aka yada ta gidan talabijin din kasar, Misis Bachelet ta ce za ta aikewa majalisar Dokokin kasar wani kudurin doka, da zai amince a zubda ciki bisa dalilai na larura.

Shugaba Bachelet ta ce ta na son bawa mata damar zubar da ciki ne bisa dalilai guda 3, idan an yiwa mace fyade, ko kuma idan mai juna biyun na cikin hadari, ko jaririn da ke cikinta na cikin hadarin da ba zai rayu ba.

A kasar Chile dai matan da aka kama sun zubda ciki ana daure su a gidan kaso har tsahon shekaru biyar.

Misis Bachelet ta kara da cewa, haramta zubda cikin dungurugum na sanya rayuwar dubban matan kasar cikin mawuyacin hali da hadari a kowacce shekara.