Boko Haram na yunkurin shiga Maiduguri

'Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na cewa 'yan kungiyar Boko Haram na can suna kokarin kai hari a birnin da safiyar lahadi.

Wata majiya ta tsoro ta shaida wa BBC cewa maharan na kokarin kai harin ne ta bangaren Mule dake kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri.

Sai dai kuma sojijin Nijeriya na can suna fafatawa da su.

Maharan Boko Haram din sun sha yin yunkuri a baya na shiga garin, amma sojiji na dakile harin na su.

Ko a makon da ya gabata ma, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kai hari birnin na Maiduguri da Munguno, lokacinda suka kwaci garin na Munguno, amma sojoji suka dakile yunkurin da suka yi na shiga birnin Maiduguri.

Karin bayani