Jordan: Muna nan kan musayar fursuna da IS

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kasar Jordan din ta nanata wannan kudirin ne duk da kashe dan kasar Japan Kenji Goto da kungiyar ta IS ta yi.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Jordan ya yi Allah wadai da kisan.

Ita ma kasar Japan ta baiyana matukar damuwa da kashe Kenji Goto da yan kungiyar kasar musuluncin suka yi.

Firaministan kasar Shinzo Abe ya yi tur da Allah da kisan.

Jami'an Japan dai sun hada hannu da hukumomin Jordan domin ganin an sako Mr Goto da kuma matukin jirgin sama dan kasar Jordan Moaz al-Kasasbeh wanda shi ma 'yan kungiyar kasar musuluncin ke garkuwa da shi