Sudan: 'Riek Mashar zai koma kan mukaminsa'

Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yarjejeniyar za ta kawo karshen zaman doya da manjan da ake yi tsakanin magoya bayan Salva Kiir da Riek Machar.

Shugaba Salva Kiir na kasar Sudan ta Kudu da tsohon mataimakinsa Riek Machar sun sake rattaba hannu a kan wata yarjejeniya da za ta kawo karshen yakin da ake yi a kasar na shekara guda.

Sai dai har yanzu ba a bayyana abubuwan da suke cikin yarjejeniyar ba, amma ana ci gaba da tattunawa a kan batutuwan da suka shafi tafiyar da mulki tare a sabuwar gwamnati.

Wani daga cikin masu shiga tsakani a rikicin kasar ya ce yana fatan za a cimma matsaya guda a ranar Litinin.

Akwai kuma rahotannin da ba a tabbatar da su ba da ke cewar watakil Mr Machar zai koma mukaminsa na mataimakin shugaban kasa.

Bangarorin biyu dai sun gwabza yaki a watan Disanbar shekarar 2013, bayan shugaba Salva Kiir ya tsige mataimakinsa daga mukaminsa.

An yi kuma ta kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin magoya bayansu, amma hakan bai samu ba.

Sai dai dole a cimma yarjejeniyar ta karshe daga nan zuwa 5 ga watan Maris din wannan shekara.