Harin Boko Haram: Me ya faru a Baga?

An kashe mutane maza da mata da kananan yara a garuruwan Baga da Doron Baga a Nigeria lokacin da mayakan Boko Haram suka kaddamar da hari a ranar 3 ga watan Junairu. Kawo yanzu babu wanda ya san adadin wadanda aka kashe amma an tilasta wa dubban mutanen barin gidajensu inda suka tsallaka zuwa kusa da tafkin Chadi.

BBC ta gana da wasu daga cikin wadanda suka tsira a wani sansanin 'yan gudun hijira a Chadi domin bayar da bayanai kan ainihin abubuwan da suka faru a wannan ranar.

1.Boko Haram ta kaddamar da hari a Baga

Mun je barikin sojoji muka tambaye su ko me ke faruwa. Sun gaya mana cewa akwai yiwuwar 'yan Boko Haram za su kawo hari, hakan yasa muka dauki adduna da wukake domin mu kare kanmu"

Harun Muhamad, wani wanda ya tsira daga harin Baga
Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karfe 05:45 na safe a ranar Asabar 3 ga watan Junairu: Mutane da dama sun riga sun tafi yin Sallar Asuba lokacin da suka soma jin karar harbe-harbe. An kai harin farko ne tun kafin alfijir ya keto.

A lokacin da mayakan Boko Haram suka soma ta'adi a bangaren yammacin Baga, wasu matasa rike da "adduna" da kulake da kuma wukake suka sha alwashin kare garin. Da farko sun soma samun nasara.

Muna tura su baya tare da sojojinmu, in ji Haroun Mohammed dan shekaru 31.

Hakan ya sa mayakan Boko Haram suka gudu cikin daji.

Mun fito kwanmu da kwar-kwata domin mu yake su, in ji Dahiru Abdullahi dan shekaru 21, inda ya kara da cewar galibin mayakan Boko Haram na sanye da kayan soji irin daban-daban.

Ya kara da cewa wasu na da bakar riga, wasu kuma na sanye da rawani. Irin rawanin da 'yan tada kayar baya suke sawa domin rufe fuskarsu a cikin sahara.

Lokacin da 'yan Boko Haram suka ja da baya, mutanen Baga sun samu sa'ida amma kuma na dan lokaci ne kawai.

2.Boko Haram sun dawo

Muna gudu suna bin mu suna harbi, wasu na faduwa suna mutuwa, yayin da wasu kuma ake binsu da babura ana tattaka su suna mutuwa. Wasu kuma sun samu isa bakin tafkin Chadi"

Hadija Abakar, wata wadda ta tsira daga harin Baga
Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Bayan wasu sa'o'i, sai mayakan Boko Haram suka kara zuwa garin. A lokacin sun zo da yawansu cikin manyan motoci da babura.

Sun fito daga cikin daji da motoci kusan 20, in ji Dahiru Abdullahi.

Mutane kusan 10 zuwa 15 ne suka fito daga cikin kowacce mota. Babu yadda za a iya sanin adadin mayakan da suka shiga cikin wannan yakin, amma 'yan gudun hijirar sun ce daruruwan mayakan Boko Haram ne suka je. Sai suka ci karfin 'yan sintiri.

Sun bude mana wuta, suna ta mana ihu, in ji Dahiru Abdullahi. "Saboda muna rike ne da adduna domin kare kanmu, bamu da zabi illa mu tsere."

Haroun Mohammed ya kara da cewar mayakan Boko Haram da suka zo a karo na biyu suna da "matukar yawa", abin da ya sa kowa ya arce.

Wadanda suka tsira sun bayyana yadda mayakan Boko Haram suka yita yi wa matasa tsawa.

Suka ce ina mazan suke, ku zo ku yi fada da mu.

Saboda karfin mayakan Boko Haram din, sojojin Nigeria ma tserewa suka yi. Shaidu sun ce sun jefar da makamansu a kasa inda mayakan suka tsinci dami.

Wasu 'yan kato da gora sun tsinci wadannan makaman inda suka yaki 'yan Boko Haram, amma da 'yan Boko Haram suka ci karfinsu, sai suma suka gudu, in ji Saratu Garba, wata mahaifiyar yaro dan shekaru 20.

A lokacin da mayakan Boko Haram suka shigo cikin gari, shaidu sun ce lamari babua dadi. Mutane sun tsere ta kowacce hanya; inda wasu suka nemi mafaka a garin Doron Baga mai albarkar kifaye wanda ke gabar tafkin chadi.

3. Kama hanyar zuwa Doron Baga

Akwai wata mata wadda jaririnta ya fada cikin ruwa. Mun fito da shi muka mika mata shi ta samu biyo mu. Muma mun samu shiga jirgin ruwan, amma kuma sun ci gaba da harbinmu"

Dahiru Abdullahi, wani wanda ya tsira daga harin Baga
Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Da tsakar rana, sai mayakan Boko Haram suka soma kashe mutane inda suka fatattaki wasu daga ciki.

Sun harbe mutane har lahira, sannan suka taka wasu mutane da motocinsu a kan hanya, in ji Saratu Garba, wanda mijinta ya bace sakamakon tarzomar.

An kirga gawawwaki da dama.

Saratu Garba da sauran 'yan gudun hijira sun bayyana yadda suka ga gawawwakin mata da kananan yara da maza kwance a kasa.

Titunan Doron Bagan sun cika da gawawwaki, a lokacin da mutane ke tserewa zuwa kusa da tafkin Chadi.

Sun yita harbinmu lokacin da muka shiga cikin kwale-kwale, in ji Dahiru Abdullahi. "An harbi wani mutum da ke kusa da ni."

Mutane da dama sun tsira daga cikin hatsaniyar. Mutane da yawa sun boye, sun kuma jira na lokaci mai tsawo tare da fatan cewar mayakan Boko Haram za su tafi. Amma sai suka ki tafiya. A cikin dare, an ci gaba da jin karar harbe-harbe.

'Yan gudun hijira sun ce sun ga lokacin da ake ta kona gidaje. A lokacin suna cikin kwale-kwale, suna ta gannin hayaki a sama.

4. Tserewa zuwa tafkin Chadi

Muna kwance lokacin da muka fara jin hayaniya. An gaya mini cewa na dauki 'ya'yana na bar gida. Ban dauki komai ba baya ga tufafin da ke jikina"

Hadija Umar, wata wadda ta tsira daga harin Baga

Wasu sun bazama a cikin daji, kuma bayan kwanaki, sun isa tudun mun tsira a wasu garuruwan Nigeria. Akalla mutane 5,000 ne suka gudu zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno, in ji kungiyar agaji ta Medicines San Frontieres. Wasu sun tsere zuwa jihohin arewa wasu kuma sun tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar.

Kusan mutane 15,000 kawo yanzu sun isa zuwa Chadi, in ji hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma a yanzu haka suna jiran samun kayayyakin agaji.

Haroun Mohammed wanda a yanzu haka bai ga matarsa da 'yarsa ba ya ce "Ban sani ba ko suna da rai ko sun mutu." Shi kuwa Dahiru Abdullahi, ya ce har yanzu yana jiran labari ne a kan kaninsa.

Shi da wasu maza tara muna tare kafin sun bace mana, in ji Dahiru.

Dahiru Abdullahi na daga cikin 'yan gudun hijira 2,500 da ke samun kulawar hukumar UNHCR a wani wuri da ake kira "Dar-es-salam" wanda ke cike da kura maisuna Baga-Sola.

Mutanen Baga da Doron Baga wadanda suka tsallaka zuwa kasar Chadi a yanzu ba suda komai.

Ban da wannan kayan na jiki na, bani da komai. A haka na fita, in ji Hadija Umar, wata uwa mai 'ya'ya uku wanda aka kashe mijinta a lokacin harin.

A Ngouboua, kungiyoyin agaji sun kafa tantuna. 'Yan gudun hijira na zaune cikin mawuyacin hali, inda suke kwana a kasa cikin sanyi.

Hare-haren Boko Haram

Daruruwa

wadanda aka kashe a harin Baga - Akwai rahotanni mabambanta kan yawan wadanda suka mutu, domin babu wasu alkaluma da aka tabbatar

3700

gine-ginen da aka lalata

  • 14638 mutanen da suka tsere zuwa Chadi

  • 774 mutanen da ke tsallaka bakin iyaka a kullum

  • 5000 wadanda suka tsere zuwa birnin Maiduguri

  • 105 yaran da ba a ga iyayensu ko dangi na cikin 'yan gudun hijira a sansanin Ngouboua

AFP

5. Zarge-zarge da kuma martani

Babu yadda za a iya gane adadin wadanda aka kashe a wannan harin. Amnesty International ta ce an kashe mutane 2,000 amma kuma babu wata hujja da za a iya tabbatar da wannan ikirarin.

Shaidu sun ce an kashe daruruwan mutane, amma watakila babu yadda za a iya gane wannan adadin.

Gwamnatin Nigeria ta ki tabbatar da adadin wadanda suka mutu. Dakarun kasar sun yi watsi da adadin na Amnesty, inda suka ce " adadin wadanda suka rasu a lokacin harin bai zarta mutane 150 ba."

Amma kuma Sambo Dasuki, Mai bai wa Shugaban Nigeria shawara a kan tsaro ya ce "kasar za ta yi amfani da adadin Amnesty" saboda "babu wata kafa mai zaman kanta da ta ba da wani adadin."

Hotunan tauraron dan adama na Baga da Doron Baga da aka dauka kafin hare-haren sun nuna irin barnar da aka yi, inda aka kiyasta cewa gidaje 3,700 aka lalata, in ji Amnesty International.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A wani bidiyo da aka wallafa a intanet, wani mutumi da ke kiran kansa Abu Mos'aab Albarnawi- wanda ya bayyana kansa a matsayin 'kakakin' kungiyar Boko Haram ya ce sun kai hari a Baga ne saboda "garin na da mahimmanci ta fannin kasuwanci da kuma tsaro ga gwamnatin Nigeria".

Sun kai harin ne bayan kwace wani sansanin soji da ke shalkwatar dakarun kasa da kasa na kasashen Nigeria da Niger da Chadi da kuma Kamaru.

Jamhuriyar Niger ta janye dakarunta a sansanin a watan Nuwambar 2014, kuma Dasuki ya ce "dakarun Nigeria ne ka dai suka rage a sansanin lokacin da aka kai harin".

Mr Dasuki ya bayyana cewa makaman da Boko Haram ta kwace, sun hada da "manyan makaman atilari da bindigogi da kuma motocin yaki"

A cewarsa, hakan ya nuna cewa dakarun Nigeria na da makaman yaki: "Duk wanda ya ce ba mu da makamai, karya yake." Ya kara da cewar sojojin da suka tsere "matsorata" ne.

6. Adadin wadanda aka kashe a hare-haren Boko Haram

Ko da yake ba a tantance adadin mutanen da aka kashe a Baga ba, amma kuma 'yan Boko Haram sun hallaka mutane da dama a cikin shekaru shida da suka wuce.

Taswirar na nuna yadda ayyukan Boko Haram ke kara yaduwa, inda suka fi maida hankali a jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe - inda aka kafa dokar ta-baci tun a shekarar 2013.

Sannan kuma da yadda hare-haren suka kara muni a shekarar 2014.

Da kuma adadin fararen hula da aka kashe a hare-haren Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service