Ba zan fita daga PDP ba — Sule Lamido

Hakkin mallakar hoto google
Image caption 'Yan Najeriya na ganin Lamido ya ki barin PDP ne saboda zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa 'ya'yansa.

Gwamnan jihar Jigawa da ke Najeriya, Sule Lamido, ya shaida wa BBC cewa ba zai fice daga jam'iyyarsu ta PDP ba duk da barazanar da take fuskanta daga babbar jam'iyyar hamayya, APC.

Ranar Lahadi ne dai gwamnan ya yi ganawar sirri da gwamnan jihar Rivers Chibuke Rotimi Amaechi, dan jam'iyyar APC kuma wanda ke matukar sukar shugaban kasar Goodluck Jonathan.

Hakan dai ya sa wasu na ganin cewa Sule Lamido na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar ta APC ne.

Sai dai gwamna -- wanda shi ne daraktan yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan a shiyyar arewa maso yammacin Nigeria -- ya ce babu abin da ya hada gawanar da suka yi da batun sauya sheka.

'Yan kasar da dama dai na ganin gwamna ya ki fice wa daga jam'iyar ta PDP ne saboda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC tana tuhumar 'ya'yansa da zargin cin hanci da rashawa, lamarin da ya sa sau da dama tana kama su.