2015: Musulmi da Kiristoci sun gana a Kano

Image caption Hukumar zaben kasar ta yi kira a guji magudin zabe

Kungiyoyin mabiya addinin musulunci da na kiristaci sun yi wani taro a Kano da ke Najeriya kan yadda za a kaucewa aukuwar rikici a lokutan zabukan watan gobe.

Kungiyon sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya ta zaman lafiya yayin zabukan.

Taron dai wani bangare ne na matakai daban-daban da ake dauka don ganin an gudanar da zabukan lafiya.

Bangarori daban-daban dai sun sha yin kira a gudanar da zaben cikin lumana.

Bayan zabukan 2011, an kashe mutane da dama tare da barnata dukiyoyi masu dinbim yawa a wasu jihohin arewacin Nigeria.