Nigeria: Ma'ikatan lafiya sun janye yajin aiki

Ministan lafiya a Nigeria Halliru Alhassan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ma'aikatan lafiyar sun shafe watanni biyu su na yajin aikin.

A ranar Talata ne ma'aikatan lafiya na Najeriya za su koma bakin aiki bayan kwashe watanni fiye da biyu suna yajin aiki, abin da ya jefa sashen kiwon lafiya na kasar cikin mummunan hali.

Hadaddiyar kungiyar ma'aikatan kiwon lafiya ta kasar ce ta bayar da sanarwar janye yajin aikin.

Shugaban kungiyar, Comrade Ayuba Waba, ya ce sun janye yajin aikin ne sakamakon ganawar da suka yi da shugaban kasar, Goodluck Jonathan, wanda ya yi alkawarin biyan bukatunsu.

Ya kara da cewa sun kuma duba kiraye-kirayen da shugabannin addinai da sarakuna suka yi musu na su duba halin da al'uma ke cikin a asibitoci, su janye yajin aikin saboda mummunan halin da marasa lafiya ke ciki.