Kungiyar IS ta kona dan Jordan da ransa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kasar Jordan sun nemi kungiyar IS ta sako Moaz kafin ta kashe shi

Wani bidiyo da kungiyar masu jihadi ta IS ta fitar, ya nuna matukin jirgin sama dan kasar Jordan, Moaz al-Kasasbeh an kona shi da ransa.

Ko da yake babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da sahihancin bidiyon, amma an nuna hoton wani mutumi tsaye a cikin keji kafin an cinna masa wuta.

An kama laftanar Moaz al-Kasasbeh a kusada birnin Raqqa na Syria a cikin watan Disamba lokacin da jirginsa ya fado kasa.

Kafar talabijin a kasar Jordan ta tabbatar da mutuwar amma ta ce kusan wata guda kenan da aka kashe shi.

A ranar Talata aka saka bidiyon a intanet sannan aka rarraba shi a shafin farfaganda na IS a Twitter.

Bidiyon mai tsawon mintuna 22, ya nuna yadda dan kasar Jordan din yake daure sannan kuma aka nuna masa bindiga.