2015: Ba za a rufe makarantun Nigeria ba

Image caption Malam Shekarau ya ce ba za rufe makarantu ba.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za a rufe makarantu ba a lokutan da za a gudanar da manyan zabukan kasar.

Ministan harkokin Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau, ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa jami'an tsaro za su samar da cikakken tsaro a lokutan zabukan don haka babu bukatar rufe makarantun.

'Yan kasar da dama dai na dari-darin cewa ya kamata a rufe makarantun saboda yiwuwar barkewar rikici a lokutan zaben.

Sai dai Malam Shekarau ya ce bai kamata mutane su rika yin tunanin aukuwar rikicin ba, yana mai cewa a baya an gudanar da zabukan ba tare da rufe makarantu ba.

Tuni dai wasu makarantun suka bayar da hutu gabanin zaben.

Za a gudanar da zabukan ne a ranakun 14 da 28 ga watan Fabrairu na shekarar 2015.

Sau da dama dai 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare a kan makarantu, musamman a arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.