Za a yi wa mutane 230 daurin rai da rai a Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A Masar daurin rai da rai daidai yake da shekaru 25 a gidan sarka

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu mutane 230 bisa zanga-zangar kin jinin gwamnati.

An yanke wa wani mai fafutuka, Ahmed Douma tare da wasu mutane 229 saboda rawar da suka taka a lokacin juyin-juya halin da ya kai ga hambarar da Hosni Mubarak.

Kotun ta tuhumi Douma da laifukan tayar da tarzoma da ingiza mutane da kuma kai hari kan jami'an tsaro.

Kawo yanzu hukuncin na ranar Laraba shi ne mafi girma da aka yanke kan masu fafutukan da suka jagoranci zanga-zangar da aka yi shekaru hudu da suka gabata a kasar.