Fotokol: Kamaru ta kashe 'yan Boko Haram 50

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mata ta ga gawaawakin mutane 31 a masallaci guda a Fotokol

Dakarun Kamaru sun ce sun kashe 'yan Boko Haram 50, yayin da kuma aka kashe musu sojoji shida a fafatawara da suka yi a garin Fotokol.

Ministan yada labarai na Kamaru, Issa Tchiroma Bakari ne ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters a ranar Laraba.

Ko da yake ya ce akwai yiwuwar yawan wadanda abin ya shafa ya fi hakan.

Mazauna garin na Fotokol dai sun ce maharan sun kashe mutane da dama, yayin da suka yanka wasu a gidaje da kuma masallatai.