An aiwatar da hukuncin kisa a Jordan

Sarki Abdallah na Jordan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Jordan ta ci alwashin daukar fansar kisan da aka ti wa Mu'az Kasasbeh.

Gwamnatin kasar Jordan ta zartar da hukuncin kisa kan masu tada kayar baya guda biyu da ake tsare da su.

Hakan dai wani martani ne ga kisan da mayakan IS suka yi wa matukin jirgi dan kasarta.

Daya daga cikinsu mai suna Sajida Al- Rishawi 'yar kunar bakin wake ce, wadda IS suka bukaci ayi musayar ta da matukin jirgin da suke tsare da shi.

Gwamnatin Jordan ta sha alwashin daukar fansa akan kisan da mayakan IS suka yi Mu'az al-Kasesbeh a wani hoton bidiyo mai daga hankali da aka nuna yadda suka banka masa wuta alhalin yana raye.

Daruruwan mutane ne suka fito akan titunan babban birnin kasar Aman, su na bukatar a dauki fansa kan kisan da aka yi wa laftanal-kanal Mua'az al-Kasasbeh. Kuma mahaifinsa na daga cikin wadanda sukai wannan machi, sai dai gwamnatin Jordan ta ce jinin sa ba zai tafi a banza ba.

An yankewa AL-Rishawi hukuncin kisa a shekarar 2005 saboda rawar da ta taka a harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 60.

Shi ma wani babban jigo na kungiyar al-Qaeda Ziyad Karbili da ya kashe wani dan asalin Jordan an kashe shi a yau.