Jirgin sama ya fada kogin Taiwan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fasinjoji 30 da ke cikin jirgin 'yan yawon bude idanu ne daga China

Wani jirgin sama dauke da fasinjoji fiye da 50 ya doki gefen wata gada kafin daga bisani ya fada cikin kogi a Taiwan.

Masu aikin ceto sun ce an tabbatar da akalla mutuwar mutane 25, yayin da wasu kusan 20 kuma ba a gansu ba.

Haka kuma masu aikin ceton a cikin kananan kwale-kwale sun yi ta kokarin kubutar da wasu fasinjojin da suka makale a cikin jirgin wanda ke kwance a jefensa kuma ruwa ya kusa shanye shi.

Wani faifai bidiyon da wani mai mota ya dauka ya nuna yadda jirgin TransAsia Airways ya yiwo kasa kuma fukafukinsa daya ya doki gadar, 'yan mintoci bayan ya tashi daga filin jiragen sama na Taipei.