APC ta yi zargin ana shirin dage zabe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar zabe a Nigeria ta ce ta shirya gudanar da zabukan kamar yadda aka tsara

A Najeriya, gwamnonin jam'iyyar adawa ta APC sun ce sun bankado wani yunkuri da Shugaba Goodluck Jonathan ke yi na amfani da taron majalisar koli ta magabatan kasar da zai gudana yau domin ganin an dage manyan zabukan kasar.

A karshen taron da su ka yi a Abuja, gwamnonin sun ce sun samu kofe na jawabin da mai ba shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro zai gabatar wa majalisar ta karkashin kasa.

Gwamnonin sun yi zargin cewa shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shirya gabatar wa taron bayanai masu tayar da hankali, da zai kafa hujja da su wajen sa a dage zabukan.

A cewar gwamnonin jam'iyyar ta APC, shugaban kasan ba shi da hurumin gabatar da batun a wajen taron majalisar magabatan, tunda hukumar zaben kasar ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zaben.

Wasu masharhanta na ganin fadar shugaban kasan tana matsa lamba ne akan a dage zabukan saboda fargabar da ta ke yi a game da samun nasara a zaben.