Sanya zane a sakon waya na cin kudi

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Mutane da dama kan yi amfani da zanen a sakonninsu don nuna yanayinsu

BBC ta fahimci cewa mutanen da ke amfani da zanen alamun yanayin mutum (emoticons ko emojis) a waya ko kananan kwamfutoci a sakonninsu na kar-ta-kwana na iya jawowa kansu cajin kudi mai yawa.

Alamun dai su ne irin wadanda ke nuna mutum ko yana dariya ko bacin rai ko kuka da sauransu.

Wani shafin intanet na neman rage kudin da jama'a ke biya na sayen abubuwan amfaninsu, mai suna MoneySavingExpert, a Birtaniya, ya ce ya samu korafi daga wurin mutane da yawa kan batun.

Lamarin da alamu ya fi shafar tsofaffin samfurin wayoyin salula na Samsung da kuma na Apple.

A yankin Scotland wata mata, ta biya kudin da ya kai fan dubu daya, sakamakon sanya zanen alamun yanayin mutum da ta kan yi a sakonninta na waya.

Lamarin dai yana faruwa ne sakamakon yadda wayar salular mutum ko kwamfutarsa ke sarrafa bayanin alamar, wadda ake kira emoticons ko emojis.

Wasu wayoyin musamman tsoffin yayi, suna juya alamun a matsayin sakon bidiyo(MMS), wanda sako ne da ya fi cin kudi.

Image caption Wasu daga cikin irin zane ko alamun da ake kirkira

Kwararrun sun kuma gano cewa a wasu lokutan, masu aikewa da sakonni sukan kirkiri alamunsu ta hanyar amfani da aya ko wakafi ko baka, da kuma sukan juya kamar alamomin na emoticons, da ke cin kudi da yawa.

Wasu kwarrarun sun gano cewa matsalar ba ta kamfanonin layin wayar salula ba ne, matsalar ta danganta ne daga kirar wayar.

Amma duk da haka wasu na ganin dole ne kamfanonin layin waya su dauki wani daga cikin laifin.

Haka kuma wasu shafukan irin su Facebook, wadanda ke alaka da jerin sunayen mutanen da mai shiga shafin ke mu'amulla da su(Contact) a wayar zamani (smartphone), su ma ana cajin su kudin MMS idan suka aika da rubutu mai dauke da zane.

Kwararun sun ce, domin kauce wa hakan, sai mutum ya daina sanya zane na alamar yanayin mutum, a sakonninsa na rubutu(text).

Haka kuma ya cire hadin da jerin sunayen abokan mu'amullarsa(contact) na waya da shafuka irin su Facebook.

Kwarrarun sun kuma shawarci masu waya ko kananan kwamfuta(tablets) da sauransu, da su rika amfani da tsarin aikewa da sakonnin rubutu na kyauta, kamar su Apple iMessage ko WhatsApp.