Malamai sun yi taro a kan zabe a Nigeria

Image caption A baya an samu rikice rikice lokacin zabe a Najeriya

A Najeriya, wasu shugabannin addinai daga arewacin kasar sun gudanar da taro don lalubo hanyoyin guje wa tashin hankali da ka iya biyo bayan zabukan.

Taron ya gudana ne a karkashin wata kungiya ta malaman addinin musulunci na arewacin kasar da suka shirya a babban birnin tarayya Abuja.

Daya daga cikin malaman Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce matasan da ke tayar da husuma basu da alkibla ta zamantakewar rayuwa.

Taron ya bukaci hukumomi a kasar su rika hukunta duk wanda aka samu yana neman tayar da zaune tsaye, musanman lokacin zabukan da ke tafe.