An samu wani da laifin yada tsiraici a intanet

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Kevin Bollaert yana karbar kudi wurin jama'a domin ya cire hotunan tsaraicin su

An samu wani mutum wanda yake gudanar da wani shafin intanet da ake wallafa hotunan tsiraici na ramukon gayya da laifin satar hotunan mutane da kuma cin kudin jama'a.

Kevin Bollaert yana gudanar da shafin intanet wanda mutane suke kai hotunan wasu da suke so su ba haushi, musanman masoya ko ma'auratan da suka rabu.

Mista Bollaert ya na kuma tafiyar da wani shafin wanda yake bukatar mutane su biya kudi idan suna so a cire hotunan tsiraicinsu da aka wallafa a shafinsa.

Mutumin zai fuskanci hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari idan aka same shi da aikata laifuka 27.

Sai dai lauyansa ya ce tabbas abin da ya yi ya sabawa wasu, amma dai ba laifi ba ne.

Wata mata a California wadda aka wallafa hoton ta a shafin ta ce an zubar mata da mutunci, kuma an kunyatar da ita.

Ta ce an tilasta mata barin gidan mahaifanta bayan an wallafa hotunan tsiraicinta.

Matar ta ce "Na rasa iyalai na. Suna tunanin na kawo musu abin kunya. An zubar mini da mutunci".

Matar daya ce daga cikin fiye da mutane 24 da suke ganin an tozarta su a shafin.