China ta yi watsi da zargin yin kutse

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kimanin masu mu'amala da kamfanin Anthem miliyan 80 ne aka saci bayanan su

China ta yi watsi da zargin da ake mata cewa ita ke da alhakin satar bayanai daga kamfanin inshorar lafiya na kasar Amurka, Anthem.

Bayanan mutane miliyan 80 ne aka ce an sace daga kamfanin lokacin da aka yi mushi kutse.

Masu binciken lamarin sun sahaida wa wata jaridar Amurka cewa salon da aka yi amfani da shi wajen kutsen ya yi kama da wadanda suka faru daga farko da aka dora laifin a kan China.

China ta ce zargin da ake mata rashin kan gado ne, domin ba abu ne mai sauki ba a gano daga inda aka yi kutse.

A ranar Alhamis data gabata, kamfanin Anthem wanda shi ne kamfanin inshorar lafiya na biyu a girma a Amurka, ya ce an yi mushi kutse, inda aka saci bayanan miliyoyin masu mu'amala da shi.

Idan ta tabbata adadin mutanen da abin ya shafa ya kai miliyan 80, to zai zamo lamarin satar bayanan wani kanfanin gudanar da sha'anin kiwon lafiya mafi girma da aka samu.

Masu binciken suka ce alamu sun nuna cewa China ce ke da alhakin kutsen.

Sai dai China a martaninta, ta ce zargin da ake mata ba shi da tushe balle makama.

Ta ce ''babu kan gado a ciki idan aka zarge mu batare da kwararan hujjoji ba''.

Mai magana da yawun ma'aikatar wajen China ya ce abu ne mai wahala a gano daga inda aka yi kuste, musanman idan daga wata kasa aka yi shi.