2015: Soyinka ya caccaki Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Soyinka na ganin cewa Jonathan ya gaza

Shahararren marubucin nan dan Nigeria, Farfesa Wole Soyinka, ya soki shugaban kasar Goodluck Jonathan inda ya ce bai cancanci a sake zabensa ba.

A wani jawabi a birnin Lagos, Soyinka ya ce gazawar gwamnatin kasar ta ceto dalibai 'yan matan Chibok da aka sace watanni 10 da suka wuce ya nuna cewa gwamnatin kasar na da babbar matsala.

"Ba zan zabi ko kuma na bai wa wani kwarin gwiwa ya zabi ci gaba da wannan gwamnatin ba saboda an sace dalibai fiye da 200," in ji Soyinka.

Wadannan kalaman na Soyinka babban cikas ne ga yunkurin Mr. Jonathan na neman wa'adin mulki a karo na biyu a kasar.

Mr. Jonathan dan jam'iyyar PDP na fuskantar kalubale a zaben, inda zai fuskanci Muhammadu Buhari na jam'iyyar adawa ta APC.