An tashi haikan don magance rikicin Ukraine

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption 'Yan a ware masu goyon bayan Rasha na ci gaba da kai hare hare a Ukraine

Ana kara azamar lalubo hanyoyin diflomasiyya domin kawo karshen rikicin gabashin Ukraine, inda shugabannin Faransa da Jamus suka gabatar da sababbin kudurori a Kiev.

Babu dai cikakken bayani game da kudurorin wadanda shugaba Francois Hollande da Angela Markel zasu tattauna su da shugaban Rasha.

Wasu rahotanni sun ce akwai yiwuwar kudurorin su nemi a bullo da sabbin hanyoyin tsagaita wuta da suka sha banban da yarjejeniyar Minsk.

Ci gaba da kazancewar rikicin Ukraine din, ya sa ana ta yin kiraye kiraye a Amurka na aikewa da makamai yankin.

Sai dai Ministan tsaron Jamus, Ursula Von Der Leyen ta ce aikawa da makamai Ukraine zai kara dagula lamarin ne kawai.