Zan takura wa masu cin amanar kasa -Buhari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Janar Buhari ya taba rike mukamin shugaban kasa a Najeriya

A Najeriya, dan takarar shugaban kasa a zaben da ke tafe karkashin jam'iyyar APC ya ce yana nan a kan bakarsa na hana masu cin amanar kasa sakat idan ya samu nasara a zaben.

Janar Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC cewa matsalolin cin hanci da rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki su suka hana Najeriya ci gaba.

Dan takarar ya ce idan ba a magance matsalar cin hanci ba, matsalar zata kashe Najeriya.

Sai dai ya ce ba abu ne mai yiwuwa ba a kama duk kan mutane da suka sace dukiyar talakawa saboda matsalar ta zamo ruwan dare, amma kuma hakan ba yana nufin sun ci bulus bane.

Janar Buhari ya sha alwashin magance matsalar rashin bin doka, inda ya yi gargadin cewa duk mai so ya zauna lafiya to ya bi doka.

Kazalika, dan takarar ya ce zai magance matsalar Boko Haram a Najeriya.