An dage zaben shugaban kasa a Najeriya zuwa watan Maris

Prof Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar zaben Nigeria, Prof Attahiru Jega

Hukumar zaben Nigeria INEC ta dage zaben shugaban kasar zuwa ranar 28 ga watan Maris saboda dalilai na rashin tsaro da wasu sassan kasar ke fama da shi.

Shugaban hukumar, Farfesa Attahiru Jega ya sanar da hakan a wani taron 'yan jarida a Abuja.

Ya ce haka zalika, hukumar ta sauya jadawalin zaben gwamnoni zuwa ranar 11 ga watan Afrilu.

Farfesa Jega ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa shawarorin da hukumomin tsaro suka bayar cewa ba zasu iya tabbatar da tsaron rayukan jama'a ba lokacin zaben.

Ya ce hukumar zaben ta shirya a gefenta, amma harkokin zabe sun hada da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da jami'an tsaro.

Farfesa Jega ya ce ya zamo wajibi su dauki shawarar hukumomin tsaron saboda kare rayukan ma'aikatanta dubu 600, da kuma masu kada kuri'a.

Wannan ganawa ta zo ne bayan ganawar da Majalissar Kasa ta yi ranar alhamis inda aka shafe awa bakwai ana tattaunawa akan batun zaben.