2015: Buhari ya bukaci mutane su yi hakuri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janar Buhari ya ce ba za a yarda da katsalandan ba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan Nigeria sun kwantar da hankalinsu kuma su gujewa tashin hankali saboda jinkirta zabukan kasar.

Buhari ya ce "Rikici zai iya kara dagula kalubalen tsaron da ake fuskanta a Nigeria kuma ya bai wa masu yunkurin yin kafar angulu a tsarin siyasa damar cimma burinsu."

A ranar Asabar, hukumar zaben Nigeria-INEC ta sanar dage zaben shugaban kasar daga watan Fabarairu zuwa watan Maris inda ta kara makonni shida.

A cewar Janar Buhari a yanzu dole ne a gudanar da zaben a ranar 28 ga watan Maris.

"Ina son in jaddada matsin jam'iyyarmu cewa ba zamu yarda da duk wata katsalandan a harkar zabe ba," in ji Buhari.

A waje daya kuma, sakataren harkokin wajen Biritaniya, Philip Hammond ya nuna matukar damuwa kan batun dage zaben, inda ya ce "bai kamata a yi amfani da batun tsaro a hana mutane 'yancinsu ba."