Martanin APC da PDP a kan dage zabe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya sun mayar da martani ga dage zabe

A Najeriya, gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aliyu Wammako ya ce ba komai yasa fadar shugaban kasar ta sa aka dage zaben shugaban kasar ba illa tsoron shan kaye a zaben.

Wammako ya shaida wa BBC cewa dalilan rashin tsaro da gwamnatin ta bayar, rufa rufa ce wadda kuma ba zata fidda ita daga tsanar da jama'a suka yi mata ba.

Ya ce matsalar tsaron da aka kasa magance wa cikin shekaru da yawa, ba za a iya magance ta ba a cikin makonni shida da aka kara a lokacin zaben.

Sai dai mataimakin Sakataren watsa labarai na kwamitin yakin neman sake zaban shugaba Goodluck Jonathan, Alhaji Tafida Isah Mafindi ya bayyana matakin da hukumar zaben ta dauka da cewa abu ne da ya dace.

Mafindi ya ce babu ruwan jam'iyyar PDP ko fadar shugaban kasa da dage zaben, al'amari ne na tsaro.