'Yan Majalisar Nijar na muhawara a kan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption A makon jiya ne Boko Haram ta kai hari a karon farko a Jamhuriyar Nijar.

A ranar Litinin ne 'yan majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ke yin muhawara kan ko su amince a tura sojin kasar zuwa wasu yankunan kan iyaka domin yaki da Boko Haram.

Suna yin wannan muhawara ce kwanaki uku bayan 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kai hari a karon farko a kasar.

Dubban 'yan gudun hijira ne suka tsere daga Nigeria zuwa Jamhuriyar Nijar da Chadi da kuma Kamaru, sakamakon hare-haren da 'yan Boko Haram ke ci gaba da kai musu.

A karshen makon jiya ne kasashen da ke iyaka da tafkin Chadi da Benin suka amince su samar da dakarun soji 8700 domin yin yaki da kungiyar Boko Haram.

A kwanakin baya ma kungiyar Tarayyar Africa ta bukaci a aike da dakaru 7,500 domin yaki da 'yan Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya shafi kasashen Nigeria da Niger da Chadi da kuma Kamaru.