Shekau ya yi wa dakarun kawance barazana

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shekau ya ce ba za a samu nasara a kansu ba

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya sha alwashin samun galaba a kan dakarun da aka kafa domin yaki da su.

A wani sabon bidiyo da ya fitar, Shekau ya ce dakarun kawancen ba za su yi nasara ba duk da cewa sun yi shelar kafa runduna mai sojoji fiye da 8,000.

Ya ce dakarun makwabtan kasashe da suka shiga Nigeria domin yakar Boko Haram sun yi kadan su iya samun galabar hana su gudanar da ayyukansu.

Kasashen Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma Benin sun kafa rundunar kawance domin ganin an kawo karshen ayyukan Boko Haram da ya jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali.

Rikicin Boko Haram ya janyo asarar rayukar dubban mutane a yayin da fiye da mutane miliyan uku suka rasa muhallansu.