'Yan Boko Haram sun sace mutane 20 a Kamaru

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Dakarun Kamaru na yaki da Boko Haram

Mayakan Boko Haram na Nigeria sun sace mutane kusan 20 lokacin da suka tare wata motar haya a arewacin Kamaru.

'Yan Boko Haram sun kwace motar da ke dauke da mutanen da suke kan hanyarsu ta zuwa cin wata kasuwa sannan suka yi awon gaba da su zuwa kusa da kan iyakar Kamaru da Nigeria.

Wasu rahotannin sun ce an sace mutane akalla 30 a wannan harin.

Rikicin Boko Haram a Nigeria ya bazu zuwa makwabtan kasashe kamar Nijar da kuma Kamaru.

A bara ma 'yan Boko Haram sun sace 'yan mata dalibai a Chibok su fiye da 200 kuma har yanzu ba a san inda suke ba.

Wannan tashin hankalin kuma ya janyo jinkirta zaben shugaban Nigeria daga ranar 14 ga watan Fabarairu zuwa ranar 28 ga watan Maris.