HSBC na taimaka wa attajirai kauce wa haraji

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bankin HSBC yaki maida martani a kan batun

Kwamitin Kasa da Kasa na 'yan jarida masu bincike, ya ce babban bankin nan na duniya, HSBC, ya ci ribar harkar da yake yi da masu dillancin makamai.

Haka kuma bankin ya ci riba a kan masu safarar miyagun kwayoyi da lu'u-lu'un fagagen yaki, da ma wadanda ta bayyana da sauran masu aikata laifuka na duniya.

BBC ma ta shiga cikin wannan bincike da aka yi a bangaren Biritaniya, ta kuma gano cewa bankin yana taimaka ma abokan huldarsa su kauce wa biyan milyoyin daloli na haraji.

Takardun na shekarar 2007, ya hada da bayanan 'yan siyasa da ma su aikata miyagun laifuka da kuma fitattun mutane daga fiye da kasashe 200, wadanda ke da asusun ajiya shakare da kimanin dala miliyan 120.

Wani dan jarida na jaridar Le Monde da ke Faransa, Fabrice L'Homme, ya ce sun sami bayanan asusun ajiyar ne ta hannun wani tsohon abokin cinikin bankin Herve Falciani.