Dage zabe zai taimaka wajen yakar Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ministan harkokin cikin gida, Abba Moro

Ministan harkokin cikin gida a Nigeria ya shaida wa BBC cewa yana da kwarin gwiwar za a samu gagarumin ci gaba a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram a cikin makwanni shida masu zuwa, domin samun damar yin babban zaben kasar da aka dage.

Abba Moro ya ce rundunar hadin gwiwa ta baya-bayan nan da aka kafa da kuma dakarun kasashen Chadi da Kamaru da Nijar na samun nasara a kan masu tayar da kayar bayan.

Ya ce "Idan har sojoji suka bukaci a ba su makwanni 6 domin su samar da tsaro domin gudanar da wannan aiki, ina ganin ba wani dalilin da zai sa mu yi tababar; za su shawo kan wannan kan yakin da ake yi, domin a samu gudanar da zabe ingantacce kuma cikin kwanciyar hankali."

Ya kara da cewa ba shi da tabbacin za a gudanar da zaben da babu tashin hankali a cikinsa, don haka ana bukatar a girke dakarun soji a duk fadin kasar yayin da za a gudanar da zabukan kasar.

A nata bangaren, babbar jam'iyyar Adawa a kasar wato APC, ta ce wannan mataki babban koma-baya ne ga Dimokradiyyar Nigeria.

A sabon tsarin, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin na tarayya a ranar 28 ga watan Maris sai kuma zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a ranar 11 ga watan Afrilu.